Isa ga babban shafi

Ana fargabar bacewar yara 70 saboda harin ta'addanci a babban birnin Mozambique

Kananan yara fiye da 70 ne ake fargabar bacewarsu a yankin Cabo Delgado na Mozambique bayan wasu sabbin hare-haren mayakan jihadi masu biyayya ga kungiyar IS wanda zuwa yanzu ya tilastawa mutane fiye da dubu 100 barin muhallansu.

Kasar ta fara fama da hare-haren masu ikirarin jihadi tun 2017
Kasar ta fara fama da hare-haren masu ikirarin jihadi tun 2017 AP - Marc Hoogsteyns
Talla

Kungiyoyin agaji da suka kunshi Save the children da kuma MSF na ci gaba da kokawa game da yadda hare-haren ‘yan ta’addan na Mozambique ke ci gaba da lakume rayukan kananan yara inda zuwa yanzu suka tilasta kulle makarantu 129 kamar yadda wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ke bayyanawa.

Mahukuntan Mozambique sun tabbatar da hare-haren a arewacin Cabo Delgado duk da cewa basu fitar da cikakkun alkaluman kananan yaran ba amma sun ce adadin ya haura 70 wadanda aka raba su da iyayensu tare da tasa keyarsu cikin dazuka.

A cewar mahukuntan a makwannin baya-bayan nan ne hare-haren ‘yan ta’addan ya sake tsananta inda daga karshen watan Janairu zuwa yanzu suka raba iyalai fiye da dubu 100 da muhallansu, hare-haren da suka faro tun a shekarar 2017.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da kaso 60 na wadanda hare-haren ya fi yiwa illa kananan yara ne kuma adadin na harin baya-bayan nan shi ne mafi yawa da ‘yan ta’addan na Mozambique suka taba kwashewa ta fuskar kananan yara.

Akwai dai rahotanni masu alaka da cin zarafi baya ga zartas da hukuncin kisa bisa zalinci da ‘yan ta’addan na Mozambique ke yi kan kananan yara ciki har da wadanda suka sata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.