Isa ga babban shafi

Kotu a Somalia ta yanke hukuncin kisa ga wasu ‘yan Morocco shida da ke aiki da kungiyar IS

  Wata kotun soji a arewacin Somalia ta yanke hukuncin kisa ga wasu 'yan kasar Morocco shida bisa alakarsu da kungiyar IS. Somalia dake yankin kahon Afirka ta shafe shekaru 17 tana fama da tada kayar baya karkashin jagorancin kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaeda, a daya geffen mayakan kungiyar IS na ci gaba da kai hare-hare a wasu yankunan kasar mai fama da tashin hankali.

Mayakan kungiyar Al Shebab
Mayakan kungiyar Al Shebab AFP/TOPSHOTS/STRINGER
Talla

A jiya Alhamis, mataimakin shugaban kotun soji na birnin Boosaaso na jihar  Puntland Ali Dahir yayin wani zama na kotu ya yanke hukuncin kisa ga wasu 'yan kasar Morocco guda shida bayan samun su da laifin tada zaune tsaye ta hanyar ta’addanci a karkashin kungiyar IS.

Dakarun kasar Somalia
Dakarun kasar Somalia AFP

Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 10 gidan yari kan wani dan kasar Habasha kuma dan kasar Somalia da ke da hannu a wannan shara’a.

Mai shigar da kara Mohamed Hussein ya shaidawa manema labarai cewa an kama 'yan kasar Morocco su 6 a yankin Puntland kuma an kwashe kusan wata guda ana gudanar da bincike.

Shugaban kasar Somalia Hassan Cheikh Mohammed
Shugaban kasar Somalia Hassan Cheikh Mohammed © HASSAN ALI ELMI / AFP

A shekara ta 2011 ne dakarun Tarayyar Afirka suka fatattaki kungiyar Al-Shabaab daga Mogadishu, babban birnin kasar Somalia, amma har yanzu kungiyar tana rike da yankuna da dama na yankunan karkara kuma tana ci gaba da kai munanan hare-hare kan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.