Isa ga babban shafi

AU da EU da Amurka sun yi gargadi kan fadadar rikici a gabashin Afrika

Kungiyar Tarayyar Afrika da Tarayyar Turai da kuma Amurka sun yi gargadi kan yiwuwar yakin Sudan da kuma rikicin da ke tsakanin Somalia da Habasha su iya hargitsa zaman lafiyar kasashen yankin gabashin Afrika.

Rikicin Sudan da kuma takaddamar Habasha da Somalia kan yarjejeniyar Somaliland ta birkita tsaro da zaman lafiyar yankin na gabashin Afrika.
Rikicin Sudan da kuma takaddamar Habasha da Somalia kan yarjejeniyar Somaliland ta birkita tsaro da zaman lafiyar yankin na gabashin Afrika. REUTERS - IBRAHIM MOHAMMED ISHAK
Talla

Kungiyoyin 2 da Amurka bayan ganawa da wakilcin kasashen gabashin na Afrika sun nemi gaggauta sulhuntawa tsakanin Habasha da Somalia a rikicin  da ya kunno kai bayan matakin Addis Ababa na kulla yarjejeniyar amfani da gabar ruwan yankin Somaliland matakin da ya harzuka Mogadishu.

Kiran na AU da EU da kuma Amurka a yayin taron masu ruwa da tsaki na yankin da ya gudana a birnin Kampala fadar gwamnatin Uganda sun ce ko shakka babu rikicin biyu na barazana ga tsaro da zaman lafiyar gabashin Afrika.

Tun cikin watan Aprilun bara ne aka faro yaki tsakanin dakarun Sojin Sudan da mayakan RSF lamarin da ya wargaza tsaron kasar tare da tilastawa fararen hula miliyan 7 barin matsagunansu.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya yanzu haka rikicin na Sudan ya hana yara miliyan 19 komawa makarantunsu.

A bangare guda yarjejeniyar amfani da gabar teku wadda Habasha ta kulla da yankin Somaliland mai kwarya-kwaryar 'yanci ya matukar fusata Somalia lamarin da ya sanya ta janye jakadanta daga Addis Ababa.

Rikicin ya sake tsananta ne bayan da Habasha ta sake kulla yarjejeniyar kawancen tsaro tsakaninta da yankin wanda ya sanya fargabar ta'azzaruwar takun-saka tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.