Isa ga babban shafi

Kasashen kuryar gabashin Afrika na fuskantar barkewar yinwa mafi muni - MDD

Halin kucin da yunwa da kasashen yankin kahon Afrika suka fada ,na matukar tayar da hankulan Majalisar Dimkin Duniya da wasu manyan kasashe, Yanayin da ya sa Antonio Gutteres yin kira na ganin an samar da kudaden tallafawa yankin ga baki daya. 

Fari na sake illa a Kasashe da dama na Afrika
Fari na sake illa a Kasashe da dama na Afrika Waldo Swiegers/Bloomberg via Getty Images
Talla

A jiya laraba Antonio Guterres  Sakataren Majalisar Dimkin Duniya ya yi kira ga kasashe da su gaggauta kara samar da kudade ga matasalar da ta tunkari  yankin kahon Afirka, musaman ta fari mafi muni a tarihin yankin. 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, sama da mutane miliyan 43 a kasashen Somalia, Habasha da Kenya na matukar bukatar agajin gaggawa, babban jami’in majalisar Dimkin Duniya ne ya fadar haka a wani taro dake gudana a  birnin New York na kasar Amurka, inda gwamnatocin duniya suka taru don neman tarbacen  dala biliyan 7 da nufin taimaka wa al’umar yankin na kanhon Afrika. 

Alkaluma daga majalisar dimkin Duniya na nuna cewa, Majalisar na samar da kusan  kashi 20 cikin 100 na agajin jinkai ga yankin. 

Duk da alkawuran da kasashe suka dauka  a baya, hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ta ce alkawarin da aka yi, zuwa wannan lokaci ya  kai dala biliyan 1.63,duk da haka da sauren aiki a gaban  Majalisar Dinkin Duniya da kawayen ta. 

Daga  karshe Gutterres ya bayyana cewa,  ya zama wajibi  su dau matakan da suka dace  wajen ceto wannan yanki daga fadawa cikin wani bala’I da ba a taba ganin irin sa ba a tarihi, kasancewa tun daga karshen shekarar 2020, kasashen dake yankin kahon Afirka da suka hada da Djibouti, Habasha, Eritriya, Kenya, Somaliya, Sudan da kuma Sudan ta Kudu, dukkaninsu ns fama da fari mafi muni cikin shekaru 40 da ya gabata. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.