Isa ga babban shafi

Rayukan kananan yara miliyan 10 na cikin hatsari saboda fari

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla kananan yara sama da miliyan 10 ke fuskantar barazanar tsananin yunwa a Yankin Gabashin Afirka sakamakon fari, adadin da ya zarce na miliyan 3 da aka kiyasta watanni biyu da suka gabata.

Wata mata goye da danta yayin bin layin karbar tallafin abinci a sansanin 'yan gudun hijira na wadanda rikicin Tigray ya raba da muhallansu a garin Shire da ke yankin na Tigray.
Wata mata goye da danta yayin bin layin karbar tallafin abinci a sansanin 'yan gudun hijira na wadanda rikicin Tigray ya raba da muhallansu a garin Shire da ke yankin na Tigray. © REUTERS/Baz Ratner/File Photo
Talla

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce muddin ba’a samu kudade da ruwan sama ba, yara da dama zasu mutu a yankin.

Babbar Daraktar Hukumar Catherine Russel ta bayyana matsalar a matsayin mafi muni da aka gani a cikin shekaru 40 da suka gabata, inda tace ya zama wajibi su shaidawa duniya, yayin da aka mayar da hankali Ukraine.

UNICEF ta ce tana bukatar akalla Dala miliyan 250 domin gudanar da aikin jinkai a kasashen Habasha da Somalia da Kenya da kuma Djibouti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.