Isa ga babban shafi

Sojan Somalia ya bude wuta kan Sojojin Hadaddiyar Daular Larabawa a kasar

Bayanai daga Somalia na cewa wani soja ya budewa sansanin sojoji wuta a birnin Mogasihu lamarin da yayi sanadin mutuwar sojoji biyar, ciki kuwa da har na hadadiyar daular larabawa.

Babu cikakken bayani game da alakar sojan da kungiyar Al-shabab
Babu cikakken bayani game da alakar sojan da kungiyar Al-shabab AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Bayanai sun ce sojan wanda bai jima da karbar horo daga rundunar sojin Somalia ba, ya gamu da ajalin sa bayan da jami’an suka mayar masa da martani.

Babu wani cikakken bayani game da dalilin sojan na kai wannan hari sansanin sojojin na Gordon da ke karkashin jagorancin dakarun hadadiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa sojan ya shammaci ma’aikatan ne lokacin da suka tayar da sallah lamarin da ya yi ajalin wasu daga cikin su.

Tuni dai kungiyar Al-shabab da ke da alaka da Al-Qaeeda ta sanar da daukar alhakin wannan hari ta cikin wata sanarwa da gidan radiyon Andalus na kasar ya samu, inda suka tabbatar da kisan sojoji 17 a maimakon 5 da hukumomin gwamnati suka tabbatar.

Shugaban kasar Sheikh Mahmoud a wata sanarwa da gwamnati ta fiyar ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalan sojojin da suka mutu, yana mai kara jadadda kokarin da kasar ke yi na tabbatar da tsaro.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.