Isa ga babban shafi

Ko da gaske ne an yi juyin mulki a Chadi?

An jiyo karar harbe-harben manyan bindigogi a babban birnin N'Djamena na kasar Chadi a kusa da shalkwatar babbar jam'iyyar adawar kasar, yayin da, aka fara yada rade-radin juyin mulki a kasar.

Shugaban mulkin sojin Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno
Shugaban mulkin sojin Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno © AFP - DENIS SASSOU GUEIPEUR
Talla

Tuni sojoji suka yi wa shalkwatar jam'iyyar adawar kawanya kamar yadda 'yan jaridar Kamfanin Dillancin Labarai na AFP suka rawaito.

Daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar ta PSF da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa AFP ta wayar tarho cewa, an yi amfani da babbar bindiga kirar Kalashnikov da kuma hayaki mai sa-kwalla.

Wasu bayanai na cewa, an kaddamar da hari ne kan Ofishin Hukumar Tsaron Cikin Gida a birnin N'Djamena wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana a wannan Larabar. 

Gwamnatin ta zargi 'yan adawar kasar da hannu a wannan farmakin karkashin jagorancin Yaya Dillo, jagoran 'yan adawar kasar.

Sai dai tuni aka shawo kan lamarin kamar yadda gwamnatin ta bayyana, tana mai cewa, an kama wadanda ke da hannu a harin kuma za a hukunta su.

Harin na zuwa ne bayan an cafke wani mamba a jam'iyyar ta PSF bayan an zarge shi da yunkurin kashe shugaban kotun kolin kasar kamar yadda gwamnati ta yi karin bayani

Sai dai tuni Dillo wanda ke da alaka ta jini da shugaba Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana harin kan Hukumar Tsaron Cikin Gidan a matsayin wanda aka kirkire shi domin aibata su.

Wannan na zuwa ne kwana guda da gwamnatin Chadi ta sanar cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 6 ga watan Mayu, inda shugaba Mahamat da Dillo za su fafata da juna.

Mahamat dai ya dare kan karagar mulki ne bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno wanda ya rasa ransa a yayin fafatawa da 'yan tawaye a 2021, yayin da ya shafe kimanin shekaru 30 yana mulkar kasar kafin ajalinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.