Isa ga babban shafi

Senegal: da yiwuwar a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 2 ga watan yuni

Taron tattauwar sulhu na kasa karkashin jagorancin shugaba Macky Sall ya amince da tsayar da ranar 2 ga watan Yuni a matsyin sabon lokacin da za a gudanar da zaben shugabancin kasar, wanda aka jinkirta yinsa a karshen watan Fabarairu.

Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Senegal Macky Sall AFP - AMANUEL SILESHI
Talla

Bayan matakin da taron kasar ya dauka na sanya sabuwar ranar zabe, a halin yanzu za a yi dakon kotun fasalta kundin tsarin mulkin kasar ta amince ta kuma tabbatar da ranar.

Taron masu ruwa da tsakin na Senegal ya kuma amince da shugaba sall ya cigaba da zama a karagar Mulki har sai an gudar da zaben.

A jiya Talata ne dai shugaban na Senegal ya gabatar da shirin yin afuwa ga fursunonin siyaysar da aka kama a kasar tun a shekarar 2021, domin kawo karshen rikicin siyasar da ya addabi kasar da ya barke sakamakon jinkintar gudanar da babban zaben.

Alkaluman da wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka bayyana sun ce, sama da mutane dubu 1 aka kama a shekarar 2021 sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnati da shugaban ‘yan adawa Ousmaane Sonko ya jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.