Isa ga babban shafi

'Yan sandan Kenya sun kama mutumin da ya yi kisa a Amurka

Hukumar ‘yan sandan kasar Kenya ta ce ta yi nasarar kama wanda ake zargi da  kisan budurwarsa bayan ya tsere daga hannun hukuma a Amurka. 

Des policiers kényans se mettent à couvert, après une explosion au centre commercial Westgate, ce lundi 22 septembre à Nairobi.
Des policiers kényans se mettent à couvert, après une explosion au centre commercial Westgate, ce lundi 22 septembre à Nairobi. REUTERS/Siegfried Modola
Talla

 

Hukamar ’yan sandan ta tsare mai laifin ne Kevin Kang’ethe da zummar mika shi Amurka dangane da kisan budurwar tasa Margaret Mbitu wacce aka samu gawarta a sashin ajiyar motoci na filin jiragen sama a shekarar da ta gabata.

Hukamar ‘yan sandan ta kara da cewa sun kama shi a hannu kuma yanzu haka yana karkashin kulawarsu a Nairobi fadar gwamnatin kasar, a cewar babban jami’in ‘yan sanda Adamson Bungei  kamar yadda ya shaidawa kamfanin dillancin labarun Faransa AFP.

Jami’in ya kara da cewa sun samu nasarar kama Kang’ethe ne bayan wani zuzzurfan bincike da suka gudanar a yayin da ya tsere daga matsugunin dangin sa da aka sanshi a cikin birnin Nairobi.

Kuma a yanzu haka zasu gurfanar da shi a gaban kotu domin amsa tuhumar tserewar da yayi daga hannun jami’an tsaro, kafin daga bisani a mika shi ga hukumomin kasar Amurka wadda ke nemansa ruwa a jallo.

Hukumomin Amurka da na Kenya sun kaddamar da farautarsa ne bayan da aka samu Mbitu a mace a sanadiyyar daddaba mata wuka da aka yi a sashin ajiye motoci na filin jirgin sama na Logan a Boston tun a watan Nuwambar shekarar da ta gabatar.

An bayar da umarnin kama Kang'ethe ne bayan da ya gudu daga Amurka zuwa kasarsa ta Kenya, inda aka kama shi a karshen watan Janairu.

‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin, wanda kafafen yada labarai daban-daban suka ce yana da shekaru 40, ya tsere ne a yayin da aka fito da shi daga dakinsa domin ya gana da lauyansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.