Isa ga babban shafi

ECOWAS ta tura tawaga Senegal bayan Amnesty ta yi suka kan murkushe masu bore

Kungiyar ECOWAS ta aike ta tawaga ta musamman zuwa Senegal don tattaunawa da mahukuntan kasar game da halin da ake ciki biyo bayan rikicin siyasar da ya dabaibayeta tun bayan sanar da matakin dage babban zaben kasar daga watan da muke ciki na Fabarairu zuwa Disamban shekarar nan.

Zuwa yanzu mutane 3 suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata a bangare guda jami'an tsaro suka kame wasu da dama.
Zuwa yanzu mutane 3 suka mutu yayinda wasu da dama suka jikkata a bangare guda jami'an tsaro suka kame wasu da dama. © AFP / GUY PETERSON
Talla

Aikewa da tawagar ta ECOWAS na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar Amnesty International ta yi gargadin cewa mahukuntan na Senegal na take hakkin al'ummar kasar musamman wadanda ke adawa da gwamnati bayan matakin Macky Sall na dage zaben kasar.

Cikin wata sanarwa da Amnesty International ta fitar dangane da halin da ake ciki a kasar ta yammacin Afrika, ta yi kakkausar suka kan matakan da jami'an tsaron kasar ke dauka wajen murkushe masu zanga-zangar.

Shugaban kungiyar ta Amnesty International a Senegal Seydi Gassama ya ce abin takaici ne yadda mahukuntan kasar ke take hakkin masu boren.

Zuwa yanzu mutane 3 suka rasa rayukansu yayinda aka jikkata wasu gommai baya ga kame daruruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.