Isa ga babban shafi

'Yan awaren Mali sun cire shingayen da suka dasa akan hanyoyin kasar

'Yan awaren Abzinawa sun sanar da cire shingen da suka kafa a manyan tituna a arewacin Mali tun a watan Disambar bara bayan da sojojin kasar suka kwace ikon garuruwa da dama.

'Yan tawayen Abzinawa a garin Kidal arewacin Mali
'Yan tawayen Abzinawa a garin Kidal arewacin Mali REUTERS/Cheick Diouara
Talla

A cewar yan awaren Abzinwan an dage duk wasu shingaye da aka sanya a kan hanyoyin da ke kan iyakar Aljeriya zuwa garuruwan Timbuktu da Gao.

Kungiyoyin 'yan tawayen da ke karkashin ikon Azbinawa sun rasa iko da yankuna da dama a arewacin kasar bayan wani farmakin da sojoji suka kai a karshen shekarar 2023 wanda ya kai ga kwace Kidal wanda nan ne sansanin 'yan awaren.

A watan Agustan da ya gabata ne aka sake samun bullar rikici a yankin, bayan shafe shekaru takwas cikin kwanciyar hankali, yayin da bangarorin biyu ke fafutukar karbe sansanonin sojin kasar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi watsi da su bisa umarnin gwamnatin Mali.

Sojoji sun kwaci mulkin kasar a shekarar 2020, kuma suna ci gaba da samun nasara, sai dai ‘yan tawayen ba su mika wuya ba inda suka fantsama cikin tsaunukan yankin.

A cewar 'yan tawayen, sojojin kasar Mali suna samun goyon bayan dakarun Wagner na kasar Rasha, sai dai gwamnatin kasar ta musanta hakan.

A cikin watan Disambar da ya gabata ne 'yan tawayen suka sanar da datse duk wasu hanyoyi domin shigo da kayayyaki da ababen hawa a arewacin kasar da ke da karancin jama'a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.