Isa ga babban shafi

Babu wanda ke mutuwa a Habasha saboda yunwa - Abiy

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya musanta rahoton mutuwar daruruwan mutane saboda yunwa a yankunan kasar da suka yi fama da matsalolin fari da rikice-rikice a shekarun baya bayan nan.

Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed
Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed AP - Mulugeta Ayene
Talla

A watan Janairu wani rahoton jami’an gwamnatin Habasha ya ce kusan mutane 400 yunwa ta kashe a yankunan Amhara da Tigray.

Sai dai a cewar Fira Ministan, ba shakka za iya samun hasarar rayuka amma fa hakan na alaka ne da cututtuka masu nasaba da rashin abinci mai gina jiki.

Kalaman Abiy Ahmed sun zo ne jim kadan bayan wani gargadin kwararrun na dabam, da ya ce adadin mutanen da ke fama da matsalar karancin abinci a Habasha na iya kaiwa kusan miliyan 11 nan a tsakanin watannin Yuli da Satumban wannan shekara.

Wannan ce ta sanya gwamnatin kasar ware sama da Dala miliyan 125 domin tallafa wa wadanda suka yi fama da matsalar karancin saukar ruwan sama da kuma rikice rikice a yankunan na Amhara da Tigray.

A ranar Litinin ne kuma, Birtaniya ta sanar da nata tallafin na dala miliyan 125 ga kasar ta Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.