Isa ga babban shafi

Matsananciyar yunwa ta kashe mutane 400 a yankin Tigray na Habasha -rahoto

Hukumar kare hakkin dan adam ta Habasha ta bayar da alkaluman da ke nuna yadda tsananin yunwa ya kashe kusan mutum 400 a yankunan Tigray da Amhara cikin watannin baya-bayan nan.

Tsananin yunwa na ci gaba da ta'azzara a yankin Tigray na Habasha.
Tsananin yunwa na ci gaba da ta'azzara a yankin Tigray na Habasha. AP - Ben Curtis
Talla

Duk da yadda gwamnatin Habasha ke ci gaba da musanta duk wani rahoto mai alaka da tsanantar yunwa a sassan kasar, ofisoshin shiyya na hukumar kare hakkin dan adam na ci gaba da bankado yadda fararen hula ke ci gaba da rasa rayukansu sanadiyyar yunwar.

Babban ofishin hukumar da ya aike da tawaga ta musamman zuwa Amhara da Tigray masu fama da fari sun gano yadda matsalar karancin abinci ke ci gaba da ta’azzara.

A cewar ofishin cikin watanni 6 da suka gabata tsananin yunwar ya kashe mutane 351 a Tigray baya ga wasu 44 a Amhara.

Ofishin ya ce wannan adadi na matsayin iya wanda aka iya tattara alkalumansu walau a asibitoci ko cibiyoyin rarraba abinci, wanda ke nuna akwai tarin fararen hular da yunwar kan kashe a gidajensu ba tare da an iya tattara alkalumansu ba.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu kalilan daga al’ummar ta yankin Amhara ne kadai ke iya samun tallafin abinci har zuwa yanzu duk kuwa da yadda masu bayar da tallafin suka dawo da aikinsu fiye da wata guda da ya gabata.

A cewar cibiyar rarraba abinci ta yankin Tigray da ke karkashin kulawar shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya da mahukuntan Habasha, kashi 14 na yawan al’ummar yankin miliyan 3 da dubu 200 ne kadai ke iya samun tallafin abinci da ake shiga da shi yankin.

Matsalar karancin abincin sakamakon fari na ci gaba da tsananta a yankunan na Amhara da Tigray wanda ya jefa miliyoyin al'ummar yankunan a matsanancin hali.

Tun gabanin wannan hali da yankunan biyu suka shiga, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin fuskantar matsananciyar yunwa a Habasha wadda ta yi fama da karancin ruwan sama tsawon shekaru 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.