Isa ga babban shafi

An zargi 'yan sanda da dukan masu zanga-zanga a yankin Tigray na Habasha

‘Yan sanda a yankin Tigray da ke fama da rikici a kasar Habasha sun kame tare da tuhumar shugabannin ‘yan adawa da magoya bayansu gabanin zanga-zangar da aka shirya yi ranar Alhamis.

Wasu mambobin kungiyar 'yan tawayen Tigray kenan, yayin wata zanga-zanga.
Wasu mambobin kungiyar 'yan tawayen Tigray kenan, yayin wata zanga-zanga. AP - Themba Hadebe
Talla

Gamayyar jam'iyyun adawa uku sun yi kira da a gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin rikon kwarya a yankin karkashin jagorancin kungiyar ‘yan tawayen Tigray, wacce ta mamaye siyasar Habasha kusan shekaru talatin har zuwa shekara ta 2018.

Hailu Kebede, wani babban jami'i a jam'iyyar SaWeT, ya shaidawa AFP cewa jami'an tsaro sun tarwatsa taron mutane ta hanyar duka da kamawa.

Jami’an ‘yan sanda da dama sanye da kayan sulke sun jefa barkonon tsohuwa a wurin taron, wanda ya gudana a karamin dandalin Romanat da ke tsakiyar birnin Mekele, kamar yadda wani dan jaridar kasar ya shaida wa AFP.

"Sun yi ta duka masu zanga-zangar da suka yi kokarin samun damar shiga," bayan sun " kama wadanda suka shirya," in ji shi.

'Yan sanda da dama ne aka girke a cikin birnin kuma dukkan hanyoyin da ke zuwa Mekele an rufe su, an kuma rufe wuraren kasuwanci.afhab

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.