Isa ga babban shafi

MSF ta bukaci dawo da baiwa Habasha agajin abinci sakamakon tsanantar yunwa

Kungiyar likitocin kasa da kasa ta Medecins sans Frontieres MSF ta bukaci gaggauta dawo da aikin bayar da agajin abinci a Habasha wanda Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka dakatar a watan Mayun da ya gabatar, sakamakon abin da kungiyar ta kira illar da matakin ke ci gaba da haifarwa a sassan kasar.

Matsalar yunwa sakamakon katse tallafin abincin na Majalisar Dinkin Duniya ya fi tsananta a yankin Tigray.
Matsalar yunwa sakamakon katse tallafin abincin na Majalisar Dinkin Duniya ya fi tsananta a yankin Tigray. AFP - YASUYOSHI CHIBA
Talla

Amurka da Majalisar Dinkin Duniya sun dakatar da bayar da agajin abincin zuwa yankin Tigray a arewacin Habasha gabanin fadadawa zuwa ilahirin sassan kasar a watan jiya, bayan zargin karkatar da abincin, sai dai tuni matakin ya haddasa matsananciyar yunwa tare da kisan tarin fararen hula.

Wata sanarwa da MSF ta fitar a jiya juma’a ta ce matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki na gab da kaiwa kololuwa a sassan Habasha musamman yankin Tigray da lamarin ya fi tsananta.

MSF ta bayyana takaici da yadda matakin dakatar da bayar da agajin abincin ke ci gaba da galabaitar da mutanen da basu ji ba basu gani ba, inda cikin sanarwar ta ke bayyana cewa matsalar yunwa ko kuma rashin abinci mai gina jiki ya kai maki 15 wanda ke nuna tsananin bukatar dauki karkashin dokokin Majalisar Dinkin Duniya.

A cewar kungiyar idan har ba a dauki matakan gaggawa wajen dawo da kai agajin ba, ko shakka babu za a ci gaba da asarar dimbin rayuka musamman kananan yara.

A baya-bayan nan dai akwai rahotannin asarar dimbin rayuka wanda ake alakantawa da katse tallafin abincin wanda kashi 1 bisa ukun al'ummar Habasha suka dogara da shi don rayuwa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.