Isa ga babban shafi

MDD za ta zaftare rabin abincin da ta ke bai wa 'yan gudun hijirar Tanzania

Hukumar Samar da Abinci ta Duniya ta ce, nan da watan gobe, za a fara bai wa ‘yan gudun hijira sama da dubu 200  rabin abincin da aka saba ba su a Tanzania sakamakon rashin kudaden tallafi. 

Wasu 'yan gudun hijirar Somalia.
Wasu 'yan gudun hijirar Somalia. AFP - YASUYOSHI CHIBA
Talla

Zabtarewar abinciwanda shi ne karo na biyu da aka gani a Tanzanicikin watannin baya-bayannan, na zuwa ne bayan dauka makamancin wanann matakin a wasu kasashen duniya dai dai lokacin da Hukumar Samar da Abincin ta Majalisar Dinkin Duniya ke fuskantar matsalar karancin kudi da tsadar farashin kayayyakin abinci sakamakon yakin Ukraine. 

Hukumarta ce, tun daga shekarar 2020, aka fara rage yawan abincin da ake bai wayan gudun hijirar na Tanzania wadanda kashi 70 daga cikinsu, sun fito ne daga Burundi, yayin da sauran kason suka fito daga Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo. 

A cikin watan Maris, an rage yawan adadin abincin da ake bai wayan gudun hijirar daga kashi 80 zuwa kashi 65, yayin da a watan gobe, ake saran adadin zai sake yin kasa zuwa kashi 50 ,lamarin da zai jefa dubban yan gudun hijirar cikin mummunan yanayin fafutukar neman abincin da jikin su ke bukata. 

Yanzu haka Hukumar Samar da Abincin tce, ana bukatar akalla dala miliyan 21 cikin gaggawa domin kaucewa sake rage adadin abincin nayan gudun hijirar. 

 An taba daukar irin wannan matakin na rage abincinyan gudun hijirar a kasashen Habasha da Sudan ta Kudu da kuma Kenya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.