Isa ga babban shafi

Amurka ta dakatar da tallafin abincin da ta ke bai wa Habasha

Amurka ta sanar da dakatar da dukkanin tallafin abincin da ta ke baiwa Habasha karkashin kungiyar USAID sakamakon wani bincike da ya gano yadda aka karkatar da tarin abincin da ta ware don agazawa miliyoyin mutanen da ke fama da yunwa a kasar.

Akwai dai zargin karkatar da tallafin abincin na Habasha.
Akwai dai zargin karkatar da tallafin abincin na Habasha. Kabir Dhanji - WFP / Kabir Dhanji
Talla

USAID ta bayyana cewa babu bukatar ci gaba da tallafawa Habashan, lura da yadda agajin baya isa inda aka tura, duk da yadda mutane miliyan 20 a kasar suka dogara da taimakon na Amurka.

Amurka dai na matsayin babbar mai taimakawa Habasha da kayakin jinkai ciki har da abinci da magunguna.

A cewar gwamnatin Amurka sun dauki matakin wanda ya ke mai matukar tsauri amma zai amfanar matuka lura da cewa babu zabi ganin yadda taimakon ke tafiya inda ba nan aka tura shi ba.

Har zuwa yanzu dai walai kungiyar USAID ta Amurka ko kuma shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya bas u iya gano masu hannu a karkatar da abincin ba.

Miliyoyin al’ummar Habasha ne dai ke fama da matsananciyar yunwa sakamakon fari biyo bayan karancin damunar da kasar ke gani tsawon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.