Isa ga babban shafi

Gwamnatin Habasha ta sanya dokar ta baci a yankin Amhara mai fama da rikici

Gwamnatin Habasha ta ayyana dokar ta baci bayan kwanaki da aka kwashe ana gwabza fada a yankin Amhara tsakanin sojoji da mayakan sa kai na yankin.

Yadda mutane suka yi cirko-cirko kenan, bayan wani harin sama da aka kai Makele, babban birnin Tigray.
Yadda mutane suka yi cirko-cirko kenan, bayan wani harin sama da aka kai Makele, babban birnin Tigray. © AP
Talla

Sanarwar da ofishin firaminista Abiy Ahmed ta fitar, ta ce an gano cewa ya zama dole a ayyana dokar ta-baci saboda hare-haren masu dauke da makamai da ke ci gaba da karuwa a yankin.

Fadan da ya barke a yankin na biyu mafi yawan jama'a a kasar Habasha a farkon wannan mako tsakanin mayakan Fano da dakarun tsaron kasar Habasha ya haifar da asarar rayuka da dama.

Yankin ya fada cikin rashin zaman lafiya tun watan Afrilu, lokacin da hukumomin kasar suka yi yunkurin kwance damarar jami'an tsaron Amhara bayan kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru biyu ana yi a yankin Tigray mai makwabtaka da Amharan.

A shekarar da ta gabata ma hukumomi sun yi kokarin tarwatsa mayakan sa kai na Amhara da aka fi sani da Fano.

A wannan makon, mazauna yankin sun ba da rahoton fada a fadin yankin Amhara yayin da ‘yan bindiga suka kai hari kan rundunan sojoji tare da toshe hanyoyi.

An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa manyan biranen yawon bude ido biyu, Lalibela da Gondar. tare da katse kafofin sadarwa na Internet, a cewar rahotanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.