Isa ga babban shafi

An kammala kwance damarar dakaru masu dauke da makamai a Habasha

An kammala kwance damarar dakaru na musamman na wasu yankuna da aka asmar da sub a bisa ka’ida ba a kasar Habasha.Shugaban rundunar sojojin tarayyar kasar a yau lahadi  ne ya sanar da haka kwanaki goma bayan sanar da matakin da ya haifar da rikici a arewacin kasar.

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan.
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan. AP - Mulugeta Ayene
Talla

Gwamnati kasar ta sanar a ranar 6 ga Afrilu cewa za ta "sake fasalin rundunar sojin kasar ",wasu hukumomin yankuna 11 a kasar ta Habasha sun samar da rukunin sojoji da suka kafa ba bisa ka'ida ba har tsawon shekaru goma sha biyar.

Farkon aikin ya haifar da tarzoma da zanga-zanga a yankin Amhara, wanda "dakaru na musamman" ke da karfi. A ranar alhamis da ta gabata dai ne aka samu kwanciyar hankali.

Janar Birhanu Jula a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo ya ce "Ya zuwa yau, tsarin runduna ta musamman na yankin ya kawo karshe.a haka aikinsu ya kare a yankin yanzu haka a cewar sa."

Wani yankin Tigray a Habasha
Wani yankin Tigray a Habasha Getty Images - Guido Cozzi/Atlantide Phototrave

A yanzu dai hukumomi za su sanya tsofaffin sojoji na musamman cikin rundunonin sojin kasar tare da ba su horo da ya dace.

Kundin tsarin mulkin kasar Habasha ya tanadi cewa jihohi 11 na tarayyar kasar, wadanda aka zana su bisa la’akari da harshe da al’adu a kasar da ke da al’umma sama da 80, suna da cibiyoyi na kansu da kuma ‘yan sandan yankin.

Amma a cikin shekaru 15 da suka gabata, wasu jihohi - ciki har da yankin Somaliya, da ke fuskantar kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma kutse daga tsattsauran ra'ayin Islama na Al-Shabaab daga makwabciyarta Somaliya - sannu a hankali sun kafa "dakaru na musamman", ba tare da aiki da kundin tsarin mulkin kasar ba amma jama'a sun amince da su.

Wasu sun zama masu ƙarfi, kamar sojojin na musamman na Amhara waɗanda suka ba da taimako mai muhimmanci ga sojojin tarayya a lokacin yaƙin da suke yi da tawaye a yankin Tigray tsakanin ƙarshen 2020 zuwa ƙarshen 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.