Isa ga babban shafi

Aby Ahmed ya kama hanyar wargaza rundunonin da wasu jihohi suka kafa ba tare da izini ba

Firaministan Habasha Abiy Ahmed bayan gargadin cewa za a dauki matakan tabbatar da doka da oda a wasu yankunan kasar, ya sha alwashin ruguza dakarun yankin da wasu jihohi suka kafa a yau lahadi.

Firaministan Habasha  Abiy Ahmed
Firaministan Habasha Abiy Ahmed AFP - AMANUEL SILESHI
Talla

Shirin na wargaza wadanan kungiyoyi, manufar itace shigar da irin wadannan rundunonin, wadanda wasu jihohi suka kafa ba tare da izini ba, cikin rundunar sojojin tarayya, ‘yan sandan yankin ko kuma na farar hula.

Wadannan dakarun dai sun haifar da cece-kuce a baya, musamman a lokacin kazamin yakin na Tigray, inda ake zargin jami'an tsaron da ke aiki a yankin Amhara da keta hakkin bil'adama.

Wani yankin Tigray a Habasha
Wani yankin Tigray a Habasha Getty Images - Guido Cozzi/Atlantide Phototrave

Kundin tsarin mulkin kasar Habasha ya bai wa jihohi 11, da aka tsara su bisa tsarin harshe da al'adu, su rika sa ido kan 'yan sandan yankin.

Amma a cikin shekaru 15 da suka gabata, a hankali wasu jihohin sun kafa runduna daban-daban, suna yin aiki ba bisa ka'ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.