Isa ga babban shafi

Ministocin Faransa da Jamus na ziyarar goyon bayan yarjejeniyar zaman lafiya a Habasha

Ministocin wajen kasashen Jamus da Faransa na ziyara a Habasha don nuna goyon bayansu ga yarjejeniyar zaman lafiyar da gwamnatin kasar ta kulla da ‘yan tawayen Tigray wanda ke kawo karshen yakin shekaru 2 da bangarorin biyu suka shafe suna yi.

Zaman kulla yarjejeniyar zaman lafiya a Habasha.
Zaman kulla yarjejeniyar zaman lafiya a Habasha. © Siphiwe Sibeko/Reuters
Talla

Ziyarar ta ministan wajen Faransa Catherine Colonna da Annalena Baerbock ta Jamus na zuwa ne kwana guda bayan ‘yan tawayen Tigray sun fara mikawa gwamnatin Habasha manyan makamansu wanda ke nuna tabbatuwar yarjejeniyar da bangariorin biyu suka cimma a ranar 2 ga watan Nuwamba.

Yayin ziyarar ta ministiocin biyu da ake sa ran su share kwanaki 2 a kasar ta kuryar gabashin Afrika za kuma su gana da Firaminista Abiy Ahmed, inda za su bayyana cikakken goyon bayan kasashensu ga zaman lafiyar Habasha.

Colonna ta bayyana cewa ziyarar wakilcin Faransar a Habasha nan una goyon bayansu ga kawo karshen yakin tare mika bukatarsu ta taimakawa wajen sake ginawa da inganta yankunan da yakin ya lalata.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ministocin za su isar da sakon Tarayyar Turai da ke fatan hada hannu da Habashan don tabbatar da zaman lafiya da kare hakkin dan adam a yankin na arewacin kasar.

Yakin na Habasha da aka faro cikin watan Nuwamban 2020 ya kashe tarin fararen hula baya tilastawa fiye da miliyan 2 barin matsugunansu a bangare guda ya bar wasu miliyoyi ba matsuguni babu kuma kayakin more rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.