Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Tigray sun fara mika manyan makamansu ga gwamnatin Habasha

‘Yan tawayen Tigray sun fara mika manyan makamansu ga gwamnati, daya daga cikin muhimman batutuwan da aka cimma tsakaninsu da mahukuntan Habasha, cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da suka kulla watanni biyu da suka gabata, domin kawo karshen kazamin rikicin da ya addabi arewacin kasar.

Wani wuri a yammacin yankin Tigray mai fama da rikici da ke kusa da garin Humera.
Wani wuri a yammacin yankin Tigray mai fama da rikici da ke kusa da garin Humera. © REUTERS/Baz Ratner
Talla

Kakakin 'yan tawayen na Tigray Getachew Reda ne ya sanar da fara mikawa gwamnati manyan makaman a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter jiya Laraba.

Sharuddan yarjejeniyar zaman lafiya da bangarorin biyu suka rattabawa hannu a ranar 2 ga watan Nuwamba, sun hada da kwance damarar mayakan 'yan tawaye, da maido da ikon gwamnatin tarayya a yankin Tigray da kuma sake bude hanyoyin sadarwa a yankin, wadanda suka katse tun tsakiyar shekara ta 2021.

Yaki tsakanin ‘yan tawaye da sojin gwamnati ya barke a yankin ne a watan Nuwamban shekarar 2020 lokacin da Firaminista Abiy Ahmed ya tura sojoji domin kame shugabannin kabilar Tigrai da suka shafe watanni suna kalubalantar ikonsa, wadanda kuma ya zarga da kai hari kan sansanonin sojin kasar.

Tun a ranar 26 ga watan Disamban da ya gabata, tawagar gwamnatin Habasha da ta hada da mai baiwa firaministan kasar shawara kan harkokin tsaro Redwan.

Hussein da wasu ministoci da dama, suka ziyarci Mekele babban birnin yankin Tigray, ziyarar da ta zama wani babban mataki a shirin samar zaman lafiyar Habasha.

Bayan 'yan kwanaki ne kuma a ranar 29 ga Disamba, 'yan sandan Tarayyar Habasha suka shiga Mekele a karon farko cikin watanni 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.