Isa ga babban shafi

Gwamnatin Habasha ta cire kungiyar Tigray daga jerin kungiyoyin ta'addanci

Majalisar dokokin kasar Habasha ta cire kungiyar ‘yan tawayen Tigray daga jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda a hukumance, wanda hakan ya kasance wani muhimmin mataki na shirin samar da zaman lafiya bayan rikicin da aka kwashe shekaru biyu ana yi a arewacin kasar.

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan.
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan. AP - Mulugeta Ayene
Talla

Matakin dai zai karfafa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a watan Nuwamban 2022 tsakanin kungiyar Tigray da  gwamnatin Habasha.

A watan Mayun 2021 ne aka sanya kungiyar ta Tigray, wacce ta taba mamaye siyasar Habasha a hukumance a matsayin kungiyar ta’addanci, wato watanni shida bayan barkewar yakin.

A lokacin wannan kazamin rikicin ne mayakan Tigrai suka shirya yin tattaki zuwa babban birnin kasar amma dakarun da ke biyayya ga Firaminista Abiy Ahmed suka yi musu luguden wuta.

Sai dai a karkashin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a Pretoria babban birnin kasar Afrika ta Kudu, kungiyar ta Tigray ta amince da ajiye makamai domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin.

Tun bayan da aka cimma yarjejeniyar ne, aka dawo da ayyukan jin kai da kuma kai kayan agaji zuwa yankin Tigray, wanda ke fuskantar matsanancin karancin abinci, man fetur, tsabar kudi da magunguna.

Samun damar zuwa yankin mai dauke da mutane miliyan shida ya kasance cikin sarkakiya a wancan lokaci, kuma ba zai yiwu a iya tantance halin da ake ciki a Tigray din ba.

Rikicin dai ya barke ne a lokacin da kungiyar ta TPLF ta kai hari kan cibiyoyin soji, inda ta fara kai wani gagarumin farmaki ga dakarun gwamnatin Abiy da ke samun goyon bayan Eritrea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.