Isa ga babban shafi

Habasha ta yi watsi da zargin HRW kan shafe kabilun yankin Tigray

Gwamnatin Habasha ta yi watsi da zargin da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi a baya-bayan nan game da yunkurin kawar da wasu kabilu a yankin yammacin kasar, wanda ta ce kanzon kurege ne.

Tigray yanki ne mai girman gaske a arewacin Habasha.
Tigray yanki ne mai girman gaske a arewacin Habasha. Getty Images - Guido Cozzi/Atlantide Phototrave
Talla

A cikin wani rahoto da aka fitar ranar 1 ga watan Yuni, kungiyar kare hakkin bil'adama ta yi ikirarin cewa, dakarun sa-kai da mayakan sa-kai daga yankin Ahmara na ci gaba da korar 'yan kabilar Tigrai da karfi daga shiyyar Tigray ta Yamma, a wani bangare na yunkurin kawar da su.

Kungiyar ta HRW ta wallafa wadannan zarge-zargen ba tare da gudanar da wani kwakkwaran bincike mai inganci a yankunan da abin ya shafa ba kuma babu wata shaida da ta goyi bayansu, in ji ma'aikatar sadarwa ta gwamnatin Habasha a cikin wata sanarwa da ta fitar.

An haramta wa 'yan jarida shiga yankin yammacin Tigray, da kuma daukacin yankin Tigray da yankin Amhara, kuma ba zai yiwu a iya tantance halin da ake ciki ba.

Gwamnatin ta ci gaba da cewa, wannan gurbataccen bayanin kan halin da ake ciki, na da nufin kawo cikas ga zaman lafiya, da rura wutar rikicin kabilanci, da hana yunkurin kasar na samar da zaman lafiya da sulhu a kasar Habasha.

Yarjejeniyar da gwamnatin Habasha da hukumomin yankin Tigrai suka rattaba hannu a watan Nuwamba a Pretoria, ta kawo karshen kazamin yakin da aka shafe shekaru biyu ana gwabzawa a arewacin kasar.

Dakarun sa-kai na Amhara da mayakan sa-kai sun goyi bayan sojojin gwamnatin Habasha yayin da suke kalubalantar ‘yan tawayen Tigray, kuma a farkon yakin, sun karbe iko da yammacin Tigray, yankin da ke da alaka da Kabilar Tigray yayin da ‘yan kabilar Amhara suna daukar yankin ne a matsayin kasar kakanninsu.

Yammacin Tigray na daya daga cikin muhimman batutuwan da yarjejeniyar Pretoria ba ta warware ba.

Dakarun na Amhara sun bayyana lamarin a matsayin barazana, yayin da hukumomin Tigrayan ba su da niyyar barin wannan yanki.

Gwamnati ta yi nuni da cewa ta fara wani tsarin tuntuba da nufin kafa kwamiti na musamman da zai rika bibiyar bangarorin, kamar yadda yarjejeniyar Pretoria ta tanada.

Sai dai tun daga wannan lokacin, gwamnatin Habasha ta ki ba wa wani kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya damar shiga arewacin Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.