Isa ga babban shafi

An sanya dokar hana fita a Habasha bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati

Hukumomi a kasar Habasha, sun sanya dokar takaita zirga-zirga a yankin Amhara, biyo bayan zanga-zangar nuna adawa da yunkurin wargaza sojojin yankin, da gwamnatin kasar ke shirin yi.

Rabon kayayyakin abinci kenan da hukumar abinci ta duniya WTF ta gudanar a Debark da ke yankin Amhara na kasar Habasha.
Rabon kayayyakin abinci kenan da hukumar abinci ta duniya WTF ta gudanar a Debark da ke yankin Amhara na kasar Habasha. AFP - AMANUEL SILESHI
Talla

An gudanar da zanga-zanga a garuruwa da dama na yankin Amhara tun bayan da gwamnatin kassar a ranar Alhamis ta sanar da shirin shigar da rundunonin soji da wasu jihohi suka kafa, cikin rundunar soja ko 'yan sanda ta tarayya.

Firaminista Abiy Ahmed ya ce an dauki matakin ne saboda hadin kan kasar Habasha, inda ya yi gargadin cewa za a dauki matakan tabbatar da doka a kan duk wanda yake addawa da matakin gwamnati.

Wadannan dakarun yankin sun haifar da cece-kuce a baya, musamman a yakin Tigray da aka dauki tsawon shekaru ana gwabzawa da su, inda wadanda ke aiki a Amhara suka ba da muhimmiyar taimako ga sojojin tarayya amma ana zarginsu da cin zarafin bil adama.

A babban birnin Gonder na Amhara, mutane da dama ne suka shiga zanga-zangar adawa da shirin gwamnati a ranar Lahadi, inda suka rika rera taken, "ba za mu yi kasa a gwiwa ba."

Hukumomi a birnin Gonder sun sanar da cewa, hukumar tsaro ta bayar da umarnin hana zirga-zirga daga karfe 8:00 na dare zuwa karfe 6:00 na safe, kuma dole ne a rufe mashaya da gidajen rawa da zarar karfe 9:00 na dare ya cika.

Kundin tsarin mulkin kasar Habasha ya bai wa jihohi 11, damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, da nufin inganta sha’anin tsaro.

Amma a cikin shekaru 15 da suka gabata, a hankali wasu sun kafa runduna ta musamman ta soji, inda ssuke gudanar da ayyuka ba bisa ka'ida ba.

'Yan kabilar Amhara su ne kabila na biyu mafi girma a kasar kuma sun dade suna zama masu fada aji a siyasance da tattalin arziki.

Yarjejeniyar zaman lafiya ta watan Nuwamban 2022 da gwamnatin Habasha, da hukumomin Tigray suka sanya wa hannu ya haifar da kakkausar suka daga al'ummar Amhara da suka shafe shekaru da dama suna fama da rikicin yankin na Tigray.

Haka zalika, rikici kan filaye kuma ya barke tsakanin kabilar Amhara da Oromo, kabila mafi girma a Ethiopa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.