Isa ga babban shafi

Al-Shabaab ta kwace jirgin shalkwaftan MDD mai dauke da mutane 5 a Somalia

Kungiyar Al-Shabaab ta kwace wanan jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin a Somaliya a jiya  Laraba bayan da ya sauka a yankin da ke hannunta bayan da ya fuskanci tangardar na'ura, a cewar wani jami’in tawagar Majalisar Dinkin Duniya.

Mayakan Al Shebab a kasar Somalia
Mayakan Al Shebab a kasar Somalia (Photo : Reuters)
Talla

Lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin ya tashi daga tsakiyar birnin Beledweyne zuwa garin Wisil da dakarun gwamnati suka  kwato kwanan nan, wanda ke cikin jihar Galmudug a wannan kasa ta Somaliya.

Mohamed Abdi Adan, ministan tsaro na jihar Galmudug, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce jirgin mai saukar ungulu ya sauka a kusa da Hindheed a yankin Galgaduud sakamakon wata matsala da aka samu.

Harin dan kunar bakin wake a Somalia
Harin dan kunar bakin wake a Somalia © AP

 

Jirgin mai saukar ungulu na dauke da fasinjoji 9 da suka hada da ma'aikatan agaji da sojoji da 'yan kwangila uku hade da wasu 'yan kasashen waje.

Majalisar Dinkin Duniya na bayar da tallafin kayan aiki da magunguna ga dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka 17,500 a Somaliya.

 

Dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya
Dakarun wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya © AFP / Mohamed Abdiwahad

Wannan halin da ake ciki na garkuwa da mutane ya bayyana irin kalubalen tsaro da ake fama da shi a Somaliya da kuma yadda kungiyoyin 'yan ta'adda irin su Al-Shabaab ke ci gaba da yin barazana, yana mai nuna bukatar hadin kan kasa da kasa domin tabbatar da tsaro a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.