Isa ga babban shafi

Sojojin Amurka sun kashe jagoran kungiyar Al-Shabab a Somaliya

Gwamnatin Somaliya ta fitar da sanarwar cewa sojojin kasar tare da na Amurka, sun samu nasarar kashe jagoran kungiyar ta’addanci ta Al-Shabab, wandda ya kitsa hare-hare da dama a kasar da kuma Kenya.

Mayakan sun jima suna kai hare-hare a wasu sassan kasar da kuma makwabtan kasashe.
Mayakan sun jima suna kai hare-hare a wasu sassan kasar da kuma makwabtan kasashe. © AFP
Talla

Ministan yada labaran kasar, Daud Aweis, ya ce an kashe Maalim Ayman, bayan wani hari na hadin gwiwa da bangarorin biyu suka kaddamar ranar 17 ga watan Disamba.

Gwamnatin Somaliya ta ce Ayman na da hannu a hare-haren ta’addanci da dama da aka kitsa a kasar da kuma wasu makwabtan kasashe.

Mai Magana da yawun dakarun wanzzar da zaman lafiya na Amurka, y ace AFRICOM sun kaddamar da harin sama a maboyar kungiyar da ke kusa da garin Jilib a kudancin Somaliya.

Ayman na daga cikin mutanen da ma’aikatar tsaron Amurka ke nema ruwa a jallo, tare da sanya ladan dala miliyan 10 ga duk wanda ya kai mata labarin inda yake.

Amurka ta ce shine yake da alhakin harin da aka kai sansanin sojinta da ke Kenya a watan Janairun 2020, inda ‘yan kasarta uku da suka kunshi jami’in soja guda da kuma wasu ‘yan kwangila biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.