Isa ga babban shafi

Sojin Somalia sun kashe mayakan al-Shabaab 55 a wata arangama tsakaninsu

Akalla dakarun Sojin Somalia 30 tare mayakan Al Shabaab 55 ne suka mutu a wata arangama da aka yi tsakanin bangarorin biyu jiya Laraba, arangamar da ke matsayin wani bangare na luguden wutar tsawon shekara guda da sojin kasar ke yi wa ‘yan ta’adda.

Wasu dakarun Sojin Somalia.
Wasu dakarun Sojin Somalia. AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Wata majiyar Soji ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, arangamar ta jiya Laraba wani bangare ne na shirin da shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya kaddamar a bara da nufin kakkabe ilahirin mayakan kungiyar na Al Shabaab da ke biyayya ga kungiyar al-Qaeda.

A cewar majiyar Sojin, Sojojin na Somalia sun kashe mayakan na al Shabaab da suka yi fito-na-fito da su akalla 55 ko da ya ke kaso mai yawa na sojojin musamman bangaren ‘yan sa kai sun kwanta dama.

Al Shabaab wadda ta faro ayyukan ta’addanci a sassan Somalia tun cikin shekarar 2006, a baya-bayan nan tana ganin gagarumin koma baya, musamman bayan kaddamar da shirin na kakkabeta a baran tsakanin Sojojin kasar da mayakan sa kai inda zuwa yanzu aka kwace tarin yankunan da a baya suka kasance a hannunta.

Sai dai wasu majiyoyi sun ce kungiyar ta sake kwace wasu yankunan bayan kaddamar da munanan hare-hare kan sojojin wanda ya kashe da dama daga cikinsu ciki kuwa har da na ketare.

Ko a watan jiya gwamnatin Somalia ta mika koke gaban Majalisar Dinkin Duniya wajen ganin an dakatar da shirin janye dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen Afrika akalla dubu 3 da ke aikin bayar da tsaro a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.