Isa ga babban shafi

Kwamitin tsaro na MDD ya cire wa Somaliya takunkumin shigar da makamai

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a a jiya Juma'a, inda ya amince da cire takunkumin shigar da makamai da aka sanyawa gwamnatin Somaliya da jami'an tsaronta, bayan shafe fiye da shekaru 30.

Zauren taron Kwamitin tsaro na MDD da ke birnin New York.
Zauren taron Kwamitin tsaro na MDD da ke birnin New York. REUTERS - MIKE SEGAR
Talla

Kwamitin mai wakilai 15, ya amince da wasu kudurori biyu da Birtaniyya ta gabatar, wanda ya kunshi cire takunkumin hana shigo da makamai da kuma na sake kakabawa mayakan al-Shabaab da ke da alaka da Al Qaeda takunkumi.

A shekara ta 1992 ce dai majalisar ta sanyawa Somaliya takunkuman shigar da makamai, bayan da kasar da ke kuryar gabashin Afirka ta fada cikin yakin basasa.

Haka nan, kwamitin ya kada kuri’ar amincewar da ficewar tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan mai fama da rikici, sakamakon bukatar hakan da mukaddashin ministan harkokin wajen kasar ya gabatar a watan da ya gabata na.

Rikici ya barke a Sudan a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata tsakanin sojojin kasar da kuma na kai daukin gaggawa RSF, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da raba dubbai da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.