Isa ga babban shafi

Al-Shabaab ta kai kazamin hari sansanin Rundunar Tarayyar Afirka a Somaliya

Mayakan kungiyar Al-Shabaab sun kai farmaki kan sansanin sojojin kasar Uganda dake karkashin rundunar AU a Somaliya ranar Jumma’a. Kawo yanzu dai ba a san ko an samu asarar rai ba a harin, wanda kungiyar dake ikirarin Jihadi dake da alaka da Al-Qaeda ta dauki alhakin kaiwa.

Mayakan Al-Shebaab a shekarar 2011
Mayakan Al-Shebaab a shekarar 2011 AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Shaidu suka de mayakan sun yi amfani da wata mota makare da bama-bamai zuwa sansanin sojin da ke Bulo Marer mai tazarar kilomita 120 kudu maso yammacin Mogadishu babban birnin kasar, lamarin da ya kai bata kashi na tsawon lokaci tsakaninsu da jami’an tsaro.

Sojojin gwamnati dake sumun goyan bayan  dakarun AU da aka fi sani da ATMIS sun kaddamar da farmaki a cikin watan Agustan da ya gabata kan kungiyar Al-Shabaab, wadda ta shafe fiye da shekaru 15 tana tada kayar baya a wannan kasa mai rauni ta kahon Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.