Isa ga babban shafi
Somalia

Somaliya ta kori babban jami'in MDD

Gwamnatin Somalia ta umarci babban Jami’in Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Nicholas Haysom ya gaggauta ficewa sakamakon zargin sa da katsalandan a harkokin cikin gida kwanaki kalilan bayan ya nuna damuwarsa kan kisan da jami’an tsaron kasar suka yi wa masu zanga-zangar da ke goyon bayan tsohon dan tawaye, Mukhtar Robow.

Babban Jami'in Majalisar Dinkin Duniya a  Somalia Nicholas Haysom
Babban Jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Somalia Nicholas Haysom hadalsame.com
Talla

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Somalia ta fitar ta ce, Haysom wanda ke wakiltar Babban magatakaddar Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Gutteress, ba zai iya ci gaba da aiki a kasar ba, sakamakon yadda ya gaza boye muradinsa na kashin kansa akan harkokin gudanarwar kasar.

A cewar sanarwar, Haysom ya keta dokokin da Majalisar ta gindaya masa a matsayinsa na babban jami’i.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, jami’an tsaron Somalia sun kashe masu zanga-zangar 15 tare da tsare kimanin 300.

Gwamnatin Somalia, ta dogara kan samun agaji daga kasashen ketare, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke ba ta kudade da kayayyakin bayar da horo ga jami’an tsaron kasar da ke yaki da mayakan al-Shebab.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.