Mutane sun mutu a kazamin harin Somalia
Akalla mutane 6 sun rasa rayukansu yayin da wasu 16 suka jikkata bayan wata mota makare da bama-bamai ta tarwatse a harabar ofishin gwamnati da ke birnin Mogadishu na Somalia.
Wallafawa ranar:
Wani babban jami’in ‘yan sanda, Ibrahim Mohamed ya bayyana cewa, motar ta yi karo da shingen bincike na jami’an tsaro a dab da shalkwatan gwamnatin yankin Hodan kafin daga bisani ta tarwatse.
Tarwatsewar motar ta rusa gine-gine da dama da suka hada da masallaci, yayin da hayaki mai kauri ya turnuke sararin samaniya.
Shaidu sun ce, an yi ta zakulo gawarwaki daga karkashin buragunzan gine-ginen da suka rushe a sanadiyar harin wanda kungiyar al-Shebaab ta dauki alhakin kaddamarwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu