Isa ga babban shafi
amurka-somalia

Amurka ta kashe mayakan Al-Shebab a Somalia

Kasar Amurka ta ce, wani harin sama da ta kai Somalia kan kungiyar Al-Shebaab ya yi nasarar kashe biyar daga cikinsu.

Al-Shebab na ci gaba da tayar da kayar baya a Somalia
Al-Shebab na ci gaba da tayar da kayar baya a Somalia AFP / M. Dahir
Talla

Rundunar Amurkan mai kula da Afrika ta sanar cewa, an kai harin ne a ranar Lahadi a kauyen El Buur da ke da nisar kilomita 235 da Mogadishu.

Sanarwar rundunar ta ce an kai harin ne da hadin-kan gwamnatin Somalia.

Wannan harin na zuwa ne a dai dai lokacin da dakarun Al-Shebaab suka kai kazamin farmaki kan dakarun Kungiyar Kasashen Afirka da ke aikin samar da zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.