Isa ga babban shafi
Somalia

Somalia: Yawan mutanen da suka hallaka ya karu

Jam'ian 'yan sanda a Somalia sun ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu a  harin da mayakan al Shebaab suka kai kan wani Otal da ke birnin Mogadishu ya karu zuwa 29.

Kofar Otal din Naso Hablod dake yankin Hamarweyne na birnin Mogadishu, a Somalia, bayan harin bam din da aka kai. Ranar 28 ga Oktoba,  2017.
Kofar Otal din Naso Hablod dake yankin Hamarweyne na birnin Mogadishu, a Somalia, bayan harin bam din da aka kai. Ranar 28 ga Oktoba, 2017. REUTERS/Feisal Omar
Talla

An shafe akalla awanni 12 ana musayar wuta tsakanin jami'an tsaron na Somalia da mayakan na al Shebaab, kafin kura ta lafa.

Da fari, wani dan kunar bakin wake ne ya afkawa kofar shiga wani otal a birnin (Naso hablod) inda wasu jami’an sojin kasar ke zaune, daga bisani kuma mayakan na al Shabaab dauke da bindigogi suka bude wuta kan otal din.

Mintuna kadan bayan faruwar hakan kuma wani bam da aka dana cikin wata mota da ke daf da tsohon ginin majalisar kasar ya tarwatse.

Makwanni biyu da suka gabata hare-haren bama-bamai kashi biyu da mayakan al Shebaab suka kai a birnin Mogadishu yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 350, mafi munin harin da kungiyar ta taba kai wa a tarihin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.