Isa ga babban shafi
Somalia

Yawan wadanda suka mutu a hare-haren Mogadishu ya karu

Yan sandan Somalia sun ce yawan wadanda suka hallaka a jerin hare-haren bam uku da aka kai a birnin Mogadishu a juma’ar da ta gabata ya karu zuwa mutane 41, yayinda wasu 106 suka jikkata.

Daya daga cikin sassan birnin Mogadushi da harin bama-bamai ya lalata.
Daya daga cikin sassan birnin Mogadushi da harin bama-bamai ya lalata. AFP / ABDIRAZAK HUSSEIN FARAH
Talla

A ranar Juma’a mayakan Al Shebaab suka tarwatsa bama-baman da aka dana a jikin wasu motoci a gaf da wani Otal da kuma cibiyar binciken manyan laifukan ‘yan sandan kasar dake Mogadishu, inda kuma suka bude wuta kan jama’a.

Mai magana da yawun ‘yan sandan kasar Ibrahim Muhd ya ce mafi akasarin wadanda suka mutu fararen hula ne, kuma kusan 20 daga ciki sun hallaka ne yayin da suke kan tafiya a motoci a dai dai lokacin da harin ya auku.

A shekarar 2011 dakarun kungiyar trayyar Afrika AU suka kori mayakan Al Shebaab daga birnin Mogadishu da suka kama, sai dai har yanzu mayakan na iko da wasu sassan kasar, inda suke ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin gwamnati jami’an tsaro da kuma fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.