Isa ga babban shafi

Akwai fargabar sabbin cututtuka su bulla daga Sudan-WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bukaci a dauki matakan gaggawa kan halin da al’ummar Sudan ke cikin na fargabar barkewar muggan cututtuka a sakamakon yakin da kasar ke yi.

Yakin ya raba mutane sama da miliyan 12 da muhallan su
Yakin ya raba mutane sama da miliyan 12 da muhallan su © AFP
Talla

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan yana mai cewa a yanzu haka cututtuka sun yi kamari a kasar ta Sudan ga kuma rashin cibiyoyin lafiya kasancewa yakin ya lalata su.

Tun barkewar yakin ranar 15 ga watan Afrilu zuwa yanzu an lalalata fiye da kaso 90 cikin 100 na cibiyoyin lafiya a kasar.

Bayanai na cewa akwai jihohin da babu ko da jibiyar lafiya guda data yi saura sakamakon yakin da ya tilastawa mutane sama da dubu 300 tserewa daga kasar.

Ta cikin wani bayani da ya wallafa a shafin sa na X Mr Tedros ya ce duniya bata da wani zabi illa taimakawa jama’ar Sudan a halin yanzu, kasancewar mata da kananan yara sune suka fi fuskantar barzanar kamuwa da cututuka wasu daga cikin su sabbi.

Yakin na Sudan ya hallaka mutane fiye da dubu 12 kamar yadda kididdigar kungiyoyin dake sanya idanu kan yadda take kasancewa a yakin irin su “Armed Conflict Location” da “Event Data Project” suka bayyana.

Majalisar dinkin duniya ta ce yanzu haka babban abinda jama’ar Sudan ke bukata shine gyara da kuma inganta cibiyoyin kiwon lafiya da yakin ya dai-daita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.