Isa ga babban shafi

Shugaban Guinea Bissau ya nada sabon Firaminista bayan yunkurin juyin mulki

Shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo ya kori Firaministan kasar tare da maye gurbinsa ba tare da bata lokaci ba, sakamakon dakile abin da ya kira juyin Mulki da ake Shirin yi masa.

Le président bissau-guinéen, Umaro Sissoco Embalo, ici lors d'une conférence de presse en Afrique du Sud en avril 2022, a annoncé la dissolution du Parlement, ce lundi 4 décembre.
Shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo kenan, yayin wani taron manema labarai, lokacin da ya kai ziyara kasar Afirka ta Kudu. © PHILL MAGAKOE / AFP
Talla

Sanarwar da fadar shugabancin kasar ta aikewa AFP, ta ce na sallami Gerald Joao Martins daga mukaminsa, tare da maye gurbinsa nan take da Rui Duarte Barros.

A watan Nuwamba ne, rikici ya barke tsakanin jami’an taro da kuma masu gadin shugaban kasa, abin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.

Embalo ya sanar da cewa an samu nasarar dakile juyin mulki, inda ya bayyana cewa ya rushe majalisun dokokin kasar, yana mai cewa kasar da ke Yammacin Afirka ta fada cikin rikici, don haka za a gudanar da zabe a fadin kasar.

Shugaban ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da kula da ma’aikatun cikin gida da na tsaro, amma Martins zai ci gaba da rike shugabancin ofishinsa.

Martins da kuma Barros dukkanin su sun kasance mambobin jam’iyyar PAIGC, wadda ta jagorancin hadakar jam’iyyun da suka lashe zaben watan Yuni.

Barros ya kasance Firaministan gwamnatin rikon kwarya tun a shekarar 2000, lokacin yana ministan kudin kasar.

Tun lokacin da Guinea Bissau ta samu ‘yancin kai daga kasar Portugal a shekarar 1974, kasar mai yawan jama’a sama da miliyan biyu ta fuskanci mabanbantan yunkuri ko kuma juyin Mulki.

An zabe shi na tsawon shekaru biyar a watan Disamba 2019, Embalo ya tsallake rijiya da baya a yunkurin juyin mulki a watan Fabrairun 2022.

Embalo wanda aka zabe shi na tsawon shekaru biyar a watan Disamban 2019, ya tsallake rijiya da baya a yunkurin juyin mulki na watan Fabrairun 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.