Isa ga babban shafi

Sojoji sun cafke mutanen da ake zargi da kitsa juyin mulki a Guinea-Bissau

Rundunar sojin Guinea-Bissau ta ce, tana tsare da shugaban sashen kula da lamuran tsaron da ake zargi na da hannu kan tashin hankalin da aka samu cikin dare a babban birnin kasar, inda ta ce lamura sun riga sun daidaita a halin yanzu.

Tun daga daren ranar Alhamis zuwa wayewar garin ranar Juma’a, aka samu musayar wuta a Bissau, yayin wani rikici da ya valle tsakanin jami’an tsaro da kuma masu gadin fadar shugaban kasa.
Tun daga daren ranar Alhamis zuwa wayewar garin ranar Juma’a, aka samu musayar wuta a Bissau, yayin wani rikici da ya valle tsakanin jami’an tsaro da kuma masu gadin fadar shugaban kasa. REUTERS - STRINGER
Talla

Tun daga daren ranar Alhamis zuwa wayewar garin ranar Juma’a, aka samu musayar wuta a Bissau, yayin wani rikici da ya balle tsakanin jami’an tsaro da kuma masu gadin fadar shugaban kasa.

Musayar wutar na zuwa ne, bayan sakin wasu manyan kusoshin gwamnati biyu da sojoji suka yi, wadanda suka amsa gayyatar ‘yan sanda domin amsa wasu tambayoyi.

Haka zalika mutanen biyu, sun amsa gayyata daga sashen shari’a na kasar a ranar da aka sako su, sai dai kuma an ci gaba da tsare su.

An dauki tsawo sa’o’I ‘yan sanda na musu tambayoyi kan yadda aka fitar da dala miliyan 10 daga asusun gwamnati, kamar yadda sashen leken asiri na rundunar sojin kasar yace ya gano.

Kasar da ke yankin Yammacin Afirka, ta fada cikin rikicin siyasa tun a shekarar 1974, inda ta fuskanci juyin mulki har sau hudu, yayin da aka yi yunkuri da dama wajen aiwatar da wani juyin mulki, amma kuma ana gaza samun nasara har yanzu.

A watan Satumba ne, shugaban kasar, Umaro Sissoco Embalo, ya nada wasu manyan Janar guda biyu, wato, Tomas Djassi, a matsayin shugaban rundunar tsaron fadar shugaban kasar da kuma Horta Inta, a matsayin shugaban ma’aikata.

Wannan sauyin da shugaban yayi, yazo ne daidai lokacin da juyin mulki a wasu kasashen Yammacin Afirka, da suka hada da Gabon, Mali, Nijar, Burkina Faso, da Guine suka auku, sai kuma Saliyo da aka yi yunkurin kifar da gwamnati a karshen mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.