Isa ga babban shafi

'Yan adawar Guinea Bissau sun samu rinjaye a zauren majalisar dokokin kasar

Kawancen 'yan adawa a Guinea-Bissau ya samu rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar, nasarar da ta basu damar kame madafun iko a zauren majalisar bayan shafe watanni 13 ba tare da yin wani tasiri ba.

Shugaban gamayyar jam'iyyun adawa na kasar Guinea-Bissau Domingos Simoes Pereira, tare da magoya bayansa.
Shugaban gamayyar jam'iyyun adawa na kasar Guinea-Bissau Domingos Simoes Pereira, tare da magoya bayansa. LUSA - ANDRÉ KOSTERS
Talla

Hukumar zaben Guinea-Bissau ta ce gamayyar jam'iyyun adawar da ake kira da ‘PAI Terra Ranka’ da ke karkashin jagorancin babbar jam’iyyar adawa ta PAIGC, sun lashe kujeru 54 daga cikin 102 a zaben ‘yan majalisar da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata.

Ita kuwa jam’iyyar shugaban kasa Umaru Sissoco Embalo ta Madem G15, ta samu kujeru 28 ne kacal daga cikin 102.

A watan Mayun shekarar bara jam’iyyar ta Madem G15 ta rusa majalisar dokokin kasar Guinea-Bissau, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Wannan sakamako dai ya kawo karshen shirin shugaba Embalo na yin gyara kundin tsarin mulki, matakin da zai shi damar dunkule madafun iko a hannunsa.

Guinea-Bissau mai al'ummar da yawansu ya kai kusan miliyan 2, ta sha fama da rikicin siyasa, inda kuma alkaluma suka nuna cewar, sau 10 aka taba juyin mulki ko kuma yunkurin juyin mulkin, tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga turawan Portugal a shekara ta 1974.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.