Isa ga babban shafi

François Bozizé ya koma Guinea-Bissau da gudun hijira daga Chadi

Tsohon shugaban Afirka ta Tsakiya, François Bozizé, ya sauya shekar gudun hijira daga Chadi zuwa Guinea-Bissau, bayan da kasar ta amince ta bashi mafaka.

Tsohon shugaban Afirka ta Tsakiya kenan, François Bozizé.
Tsohon shugaban Afirka ta Tsakiya kenan, François Bozizé. AFP/Sia Kambou
Talla

François Bozizé, wanda faduwarsa akan mulki a shekarar 2013 ya haifar da yakin basasa, ya fake ne a N'Djamena a karshen shekarar 2021, a dai dai lokacin da ake kokarin kwato mafi yawan yankunan Afirka ta Tsakiya, a hannun kungiyoyin masu dauke da makamai daban-daban da gwamnatin shugaba Faustin Archange Touadéra ta yi.

Sai dai kasancewarsa a kasar Chadi, yayin da kungiyarsa ta Coalition of Patriot for Change (CPC), babbar kungiyar 'yan tawaye, ke ci gaba da yakin neman zabe a arewacin kasar, ya haifar da dagulewar dangantaka tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna, inda gwamnatin Bangui ta zargi takwararta da ke N'Djamena da aikata laifukan yaki, da kuma barin ‘yan tawayen suyi aiki daga kasar.

Tsohon shugaban, ya bar kasar Chadi ne a ranar 3 ga Maris, bisa yarjejeniyar da aka cimma a yayin taron bangarorin uku tsakanin Angola, Chadi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a Luanda ranar 17 ga watan Fabrairu, in ji shugaban diflomasiyyar Chadi Mahamat Saleh Annadif.

Ministan ya kara da cewa, Guinea-Bissau ta amince ta ba wa tsohon shugaban mafaka, kuma yana can tun ranar 3 ga Maris.

"Bozize ya zo kasar Chadi ne bisa bukatar Angola da kuma wata yarjejeniya da aka cimma da mahukuntan Afirka ta Tsakiya," in ji Saleh Annadif.

Tsohon shugaba Bozizé, ya bar birnin N'Djamena a ranar 3 ga Maris, kamar yadda mashawarcin shugaban kasar Umaro Sissoco Embalo, ya ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.