Isa ga babban shafi

Wata sabuwar cuta ta kama masunta sama da 300 a kasar Guinea

Sama da masunta 300 ke kwance a asibiti sakamakon kamuwa da wata irin cutar fata da ba a san asalinta ba, a kasar Guinea da ke yammacin Afirka, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar ya bayyana, abin da ya sanya hukumomin kasar suka kaddamar da bincike kan lamarin.

Yadda masunta ke neman kifi a wani kogin Guinea.
Yadda masunta ke neman kifi a wani kogin Guinea. © africanews
Talla

Hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna masunta dauke da wasu irin kuraje a fuska, baki da gabobin jikinsu.

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin kasar, Ousmane Gaoual Diallo ya fitar, ya ce, gwamnati ta kafa kwamitin da zai bibiyi wannan ibtila’I daga ma'aikatun muhalli, kiwon lafiya, da kuma ruwa.

Sanarwar ta ce akwai tawagar masana kimiyya da suka dauki samfurin ruwan da ake zargin nan ne cutar ta samu asali, inda zza su gudanar da bincike a kai, a dakunan gwaji da ke kasar ta Guinea da kuma wasu kasashen da suke da kwarewa a fannin.

Binciken da aka gudanar kan kayyakin kamun kifi da masuntan da abin ya shafa suka shigo da su ya nuna cewa za a iya amfani da ssu, in ji sanarwar.

A watan Nuwamban 2020, daruruwan masunta aa Senegal sun kamu da wata cutar fata mai irin wadannan alamu, kuma ba a san inda cutar ta samo asali ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.