Isa ga babban shafi
ECOWAS - Guinea Bissau

ECOWAS za ta aike da dakaru Guinea-Bissau

Kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS za ta aike da dakaru zuwa Guinea Bissau don taimakawa wajen dawo da kasar cikin hayyacinta, biyo bayan wani yunkurin juyin mulki a farkon wannan mako.

Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO da suka fara taron gaggawa a Ghana saboda juyin mulki a yankin.03/02/2022.
Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO da suka fara taron gaggawa a Ghana saboda juyin mulki a yankin.03/02/2022. © nigeria vice president office
Talla

Bayan taron da kungiyar ta gudanar a birnin Accra na Ghana a ranar Alhamis, shugaban hukumar zartarwar ECOWAS, Jean-Claude Kassi Brou ya ce kungiyar ta yanke shawarar tura sojoji kasar Guinea Bissau ne don kare dimokaradiyya da kiyaye zaman lafiya da tsaro.

Ya ce wannan wani abu ne da za ta yi cikin hanzari don tabbatar da cewa irin wannan yunkuri na karbe mulki da karfin tuwo bai sake faruwa ba.

Sanarwar bayan taron na ECOWAS ta ce jami’an tsaron da za a tura Guinea Bissau sun hada da sojoji da ‘yan sanda da za  a turo daga Gambia, inda dakarun kungiyar ke girke tun bayan bayan zaben da ya yi sanadin saukar Yahya Jamen daga karagar mulki a shekarar 2017.

Baya ga yanayin da ake ciki a kasar Guniea Bissau, taron na Ecowas ya tattauna halin da ake ciki a Burkina Faso, Guinea Conakry da Mali.

ECOWAS ta yi ayyukan kawo zaman lafiya a Guinea Bissau a shekarun 2012 da 2020, kuma dakarunta sun bar kasar ne bayan da aka rantsar da shugaba Umaru Sissoco Embalo, sakamakon cewa da ya yi ba ya bukatar su a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.