Isa ga babban shafi
ECOWAS/CEDEAO

Shugabannin ECOWAS na gudanar da taron gaggawa kan juyin mulki a yankin

Shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma sun fara gudanar da taron su na musamman a birnin Accra dake kasar Ghana, inda ake saran su tafka mahawara dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso da kuma yunkurin da bai samu nasara ba a Guinea Bissau.

Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO da suka fara taron gaggawa a Ghana saboda juyin mulki a yankin.03/02/2022.
Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO da suka fara taron gaggawa a Ghana saboda juyin mulki a yankin.03/02/2022. © Office of the Nigeria Vice president
Talla

A makon jiya shugabannin sun gudanar da taro inda suka yanke hukuncin tura tawaga zuwa Burkina Faso domin tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.

Juyin mulkin Burkina na zuwa ne bayan wanda akayi a watan Agusta a kasar Mali, wanda kuma shine na biyu a kasar, bayan na kasar Guinea inda sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Alpha Conde.

Yayin da kungiyar ke lalubo hanyar dakile juyin mulki, sai aka samu irin wannan yunkuri na kifar da gwamnati da sojoji suka yi a kasar Guinea Bissau, matakin da ya kaiga rasa rayuka.

Ana saran taron na yau ya gabatar da matsayin sa akan halin da ake ciki a Burkina Faso sakamakon ganawar da tawagar ECOWAS tayi da shugabannin sojin kasar da kuma jaddada matsayin ta na adawa da juyin mulkin a yankin baki daya.

Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO da suka fara taron gaggawa a Ghana saboda juyin mulki a yankin.03/02/2022.
Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO da suka fara taron gaggawa a Ghana saboda juyin mulki a yankin.03/02/2022. © Office of the Nigeria Vice president

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka ta AU tare da ECOWAS duk sun dakatar da Burkina Faso bayan juyin mulkin da ya gudana a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.