Isa ga babban shafi
Mali-ECOWAS

A shirye muke mu yi sulhu da ECOWAS - Gwamnatin Mali

Shugaban Mulkin Sojin Mali, Assimi Goita ya ce, a shirye suke su yi zaman sulhu bayan Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ta kakaba wa kasar takunkumai masu tsauri saboda jinkirta gudanar da zabe a kasar.

Assimi Goita, shugaban mulkin sojin Mali
Assimi Goita, shugaban mulkin sojin Mali AFP - NIPAH DENNIS
Talla

A ranar  Lahadin da ta gabata, Kungiyatar ta ECOWAS ta amince ta rufe kan iyakokin Mali da kasashen yankin Sahel, sannan ta  kara lafta mata takunkumin hana ta kasuwanci.

Tuni Faransa, uwargijiyar Mali,  ta fito fili ta goyi bayan matakin da ECOWAS ta dauka a wani zama da ya gudana a zauren Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkiin Duniya.

Kungiyar ta ECOWAS ta kuma amince ta katse tallafin kudaden da ake bai wa Mali tare da daskarar da kadarorinta a babban bankin kasashen yammacin Afrika da kuma  sallamar jakadodinta na kasashen yankin Sahel.

Duk da cewa, shugaban mulkin sojin na Mali ya caccaki wadannan matakai, amma ya ce, kasar a shirye take ta yi sulhu  da ECOWAS.

Wannan na zuwa ne bayan sojojin na Mali karkashin jagorancin Assimi Goita sun bayyana cewa, da yiwuwar a dauki tsawon shekaru biyar kafin su shirya zabe domin mika mulki lga farar hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.