Isa ga babban shafi

Kungiyar ECOWAS ta sanyawa Mali takunkumai tare da janye jakadun ta

Taron shugabannin kasashen Yankin Yammacin Afrika Ecowas/Cedeao, ya amince da sanya wa Mali sabbin takunkumai don tilasta wa sojoji gaggauta mika mulkin kasar a hannun zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya.

Shugabanin kasashen Yammacin Afrika a Accra na kasar Ghana
Shugabanin kasashen Yammacin Afrika a Accra na kasar Ghana © Serge Daniel/RFI
Talla

wasu daga cikin matakan da taron shugabannin  kasashen ya dauka,sun hada da rufe iyakokin Mali da illahirin kasashen dake makoftaka da ita.

bayan ga haka,taron ya ce daga yanzu ba za a baiwa sojojin dake mulki a Mali damar taba kudaden da kasar ta mallak a cikin asusun ajiyarta dake babban bankin kasashe masu amfani da kudin Cfa wato BECEAO ba,sai dai kudaden da za a yi amfani da su domin sayen magunguna ko kuma wasu abubuwa na bukatar gaggawa.

Taron Shugabanin kasashen Ecowas da Uemoa
Taron Shugabanin kasashen Ecowas da Uemoa © RFI/Serge Daniel

Har ila yau taron,wanda ya hada da kungiyoyi biyu,wato Ecowas da kuma  Uemoa wato kungiyar kasashe masu amfani da takardar kudin Cfa,ya ce daga yanzu an haramta duk wata hada-hadar kudade tsakanin Mali da sauran kasashen yankin 14.

Domin nuna wa sojojin Mali cewa da gaske suke yi,kasashen na yammacin Afrika sun sanar da janye illahirin jakadojinsu daga kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.