Isa ga babban shafi

An mika tsohon shugaban Guinea Dadis Camara gidan yari bisa zargin kisa

An tura tsohon shugaban mulkin sojin kasar Guinea, Moussa Dadis Camara gidan yari, tare da wasu da ake zargi a kashe-kashen da aka yi ranar 28 ga watan Satumban 2009, kafin a bude shari'arsu ranar Laraba.

Tsohon shugaban Guine kenan, Moussa Dadis Camara,.
Tsohon shugaban Guine kenan, Moussa Dadis Camara,. AFP PHOTO / AHMED OUOBA
Talla

Salifou Beavogui, daya daga cikin lauyoyin da ke kare tsohon shugaban, ya shaidawa manema labarai a wajen kotun cewa mai shigar da kara ya kai mutane shidan zuwa gidan yari, inda da alama za a tsare su har zuwa karshen shari’ar.

Kyaftin Camara da wasu tsoffin jami’an soji da na gwamnati su 10 za su gurfana a gaban kotu ranar Laraba.

A ranar 28 ga Satumba, 2009, jami'an tsaron da ke biyayya ga shugaban mulkin sojan lokacin suka kashe mutane fiye da 150 tare da yi wa mata a kalla 109 fyade a wani gangamin siyasa da ya gudana a filin wasa na Conakry, a cewar wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya.

Dubun dubatar magoya bayan ‘yan adawa ne suka taru a filin wasan domin gudanar da zanga-zangar lumana don nuna adawa da yiwuwar zaben Camara wanda ya hau kan karagar mulki a watan Disambar 2008 kafin a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

Shaidu da dama sun ba da rahoton yadda jami’an tsaron fadar shugaban kasa, da jami’an ‘yan sanda da kuma ‘yan bindiga suka shiga filin wasan da tsakar rana, suka killace hanyoyin fita tare da bude wuta kan taron jama’a.

Masu bincike na kasa da kasa sun gano cewa an ci zarafin bil’adama sosai a wancan lokacin, lura da yadda aka shafe kwanaki da dama ana ta'addanci kan mata da maza da ake tsare da su.

A jajibirin shari’ar na ranar Laraba, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto inda ta yi kira da a bi kadin wadanda aka yi wa fyade a kasar Guinea da kuma gaggauta samar da wata cikakkiyar doka kan cin zarafin mata.

Camara, wanda ya yi gudun hijira a Burkina Faso, ya koma Conakry a daren Asabar domin gurfana a gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.