Isa ga babban shafi

Al'ummar Masar na dakon sakamakon zabe bayan shafe kwana 3 suna kada kuri'a

Al’ummar Masar na ci gaba da dakon sakamakon zaben da suka shafe kwanaki 3 suna kada kuri’a a babban zaben kasar da shugaba mai ci ke neman tazarce a wa’adi na 3.

Rahotanni sun ce an samu fitowar jama'a a zaben na bana fiye da shekarar 2018.
Rahotanni sun ce an samu fitowar jama'a a zaben na bana fiye da shekarar 2018. AP - Amr Nabil
Talla

Tun da misalin karfe 7 na yammacin jiya Talata ne aka kulle rumfunan zaben kasar bayan bude su tun ranar Lahadin da ta gabata wanda ya bayar da dama ga ‘yan kasar miliyan 67 da ke da katin zabe iya kada kuri’unsu.

Alkaluma sun nuna cewa, yanayin fitar jama’a rumfunan zabe ya banbanta da wanda aka gani yayinda zaben 2018 lokacin da kashi 41 kadai na ‘yan kasar suka kada kuri’unsu.

Kamfanin dillancin labarai na Al-Ahram ya bayyana cewa wannan ne zabe mafi ganin cikowar jama’a da ya faru a Masar.

Shugaba mai ci Abdel Fatta El-Sisi wanda shi ne tsohon hafson sojojin Masar na karawa ne da ‘yan takara 3 a zaben wadanda dukkaninsu ba fitattu ba da suka kunshi Farid Zahran jagoran jam’iyyar ‘yan mazan jiya ta ESDP sai Abdel-Sanad Yamama daga jam’iyyar Wafd kana Hazem Omar na RPP.

A ranar 18 ga watan nan ake fatan kammala fitar da sakamakon saben daga kowanne yanki na kasar kuma dole sai dan takara ya samu fiye da kashi 50 ne zai iya nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.