Isa ga babban shafi

Taron sulhu tsakanin Habasha da 'yan tawayen Oromo ya watse

Tattaunawar neman sulhun da aka yi tsakanin gwamnatin Habasha da ‘yan tawayen yankin Oromia, ta watse ba tare da an cimma wata matsaya ba, kamar yadda dukkanin bangarorin suka tabbatar a jiya Talata.

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan, lokacin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dokokin kasar da ke Addis Ababa, ranar 7 ga watan Yuli, 2022.
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan, lokacin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dokokin kasar da ke Addis Ababa, ranar 7 ga watan Yuli, 2022. AP
Talla

Karo na uku kenan da ake gaza kawo karshen kazamin fadan da aka shafe fiye da shekaru 20 ana yi tsakanin sojojin gwamnati da mayakan ‘yan tawayen na kungiyar OLA, da ke zargin an mayar da al’ummar yankin Oromia saniyar ware.

A watan Afrilun da ya gabata aka fara tattaunawar sulhun a kasar Tanzania, aka kuma sake gudanar da wani taron a watan Mayun, kafin wanda aka karkare a jiya Talata, dukkaninsu kuma ba tare da an kai ga gaci ba. 

An dauki tsawon makonni biyu ana tattaunawar nemo mafita a Tanzania, yayin da ake fama da matsalar ayyukan ta’addanci a Oromia, yanki mafi yawan jama’a a kasar Habasha.

A watan Afrilu, bangarorin biyu suka fara tattaunawar zaman lafiya ta farko, wadda itama aka Karkare ba tare da an samu nasarar cimma jituwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.