Isa ga babban shafi
TSAGERANCI

Majalisar dokokin Kenya ta amince da tura yan sanda dubu daya a Haiti.

Yan majalisar dokokin kasar Kenya sun kada kuriar amincewa da batun tura daruruwan yan sanda a kasar Haiti karkashin rundunar Majalisar Dinkin Duniya, domin taimaka wa kasar dake yankin  Caraïbes, fada da ayukan tashen hankulan da kungiyoyin yan tsagera dake dauke  makamai ke haddasawa a kasar 

Tawagar yan sandan Kenya a kokarin murkushe masu zanga zanga a birnin Nairobi a ranar  19 Yuli 2023.
Tawagar yan sandan Kenya a kokarin murkushe masu zanga zanga a birnin Nairobi a ranar 19 Yuli 2023. © Brian Inganga / AP
Talla

A watan yulin da ya gabata ne kasar Kenya ta kudiri aniyar aikawa da yan sanda dubu daya, bayan da kasar Haiti ta gabatar da rokon neman taimakon kasashen duniya na jami’an tsaro da zasu yi fada da kungiyoyin yan tsageran da ke da alhakin tada zaune tsaye a kasar 

Sai dai kuma a farkon watan octoban da ya gabata, wata jam’iyar yan adawa ta shigar da kara gaban kotu domin dakatar da batun tura yan sandan a Haiti. 

Inda ta bayyana cewa shirin bai kunshi ra’ayin al’umma ba kuma ma ya sabawa kundin tsarin mulki, domin sojoji kawai ake iya aikawa aiki a wanjen kasar ta Kenya 

Mataimakiyar shugaban majalisar dokoki, Gladys Boss, ce ta bukaci kada kuriar yan majalisar inda suka amince da tura yan sandan a Haiti tare da kare matakin da cewa bai sabawa kundin tsarin mulkin kasar kenya ba, kuma ya yi la’akari da ra’ayoyin al’ummar kasar da aka tattara tsakanin ranakun biyu zuwa 9 ga wannan wata na novemba da muke ciki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.