Isa ga babban shafi

Dan shugaban Kamaru na son gadon kujerar mahaifinsa

Dan shugaban kasar Kamaru, Franck Emmanuel Biya ya sake bayyana a fagen siyasar kasar, bayan, wacce ya yi a ranar 8 ga watan Oktoban da ya gabata, lokacin da ya yi furuci kan hadarin    Mbankolo da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 30.

Franck Biya, dan shugaban kasar Kamaru, Paul Biya.
Franck Biya, dan shugaban kasar Kamaru, Paul Biya. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

 

A jiya Lahadi a lokacin taron siyasar jam’iyar mahaifinsa ta RDPC ya fito fili ya  bayyana cewa zai gaji mahaifinsa shugaba Paul Biya da zaran ya kammala wannan wa'adin watakila.

Tuni magoya bayan jam'iyyar a Kamaru suka yi lale marhabin da matakin mai kama da fin karfi, inda suke cewa, sun gamsu da mulkin shugaba Biya.

A hirarsa da sashen hausa na RFI, Alhaji Ibrahim na Habu, daya daga cikin masu goyon bayan gwamnatin Biya a Kamaru ya bayyana shugaba Biya a matsayin mutun mai kwakwaluwa duk kuwa da tsufarsa wadda ba ta hana shi gudanar da aiki ba a cewarsa.

Wannan na zuwa ne a yayin da wasu masu rajin kare hakkin bil'adama ke korafi kan yadda wasu shugabannin nahiyar suka mayar da mulki tamkar gadon gidansu, inda uba ke mika ragama ga dansa.

Shugaban Kamaru, Paul Biya.
Shugaban Kamaru, Paul Biya. Getty Images via AFP - KEVIN DIETSCH

Shugaba Biya mai shekaru 90 da haihuwa, ya dare kan karagar mulkin Kamaru tun a ranar 6 ga watan Nuwamban shekarar 1982, inda ya shafe kimanin shekaru 41 yana jagorancin kasar, yayin da a yanzu yake shirin mika ragama ga dansa.

 

Masharhanta sun sha yin gargadin cewa, irin wannan kaka-gida kan mulki ne ke haddasa juyin mulki a kasashen Afrika kamar yadda ya faru kwanan nan a kasar Gabon, kasar da iyalan gidan Bongo suka shafe kimanin shekaru 56 suna jagorancin kasar kafin sojoji suka karbe mulki daga hannun Ali Bongo a ranar 30 ga watan Agustan da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.